Dan Maraya Jos
4.0 and up
Android OS
Over Dan Maraya Jos
Wakokin marigayi dan maraya jos
An haifi Adamu Wayya wanda aka fi sani da dan Maraya Jos a 1946, inda hakan ke nuni da cewa ya rasu yana da shekara 69 ke nan, sai dai wadansu na kusa da marigayin sun bayyana cewa ya kai shekara 80.
Mahaifin dan Maraya mawaki ne, asalinsa daga Sakkwato, inda bayan ya zo Bukur a Jihar Filato ne ya yi waka a fadar Sarkin Bukur, inda Sarki ya bukaci ya zama mawakinsa, a lokacin an zo da marigayi a goye, sai dai ba a jima ba mahafinsa ya rasu, inda kuma mahaifiyarsa ta rasu tun bai yi wayo ba, hakan ya sanya ake kiransa dan maraya.
Daga nan Sarkin Bukur ya ci gaba da rikonsa, kuma bayan ya taso ya fara sha’awar kidan kuntigi bayan ya ga makadansa a lokacin da suke hanyar wata tafiya zuwa Maiduguri.
Marigayin ya fara da ‘Wakar Karen Mota’ ne, sannan a lokacin Yakin Basasa ya rika yi wa sojojin Najeriya wakokin karfafa gwiwa a fagen daga. Sauran wakokin marigayin sun hada da ‘Wakar Jawabin Aure’ da ‘Wakar dan Adam’ da ‘Wakar Auren Dole’ da ‘Wakar Duniya’ da ‘Wakar Gulma-Wuya’ da sauransu.
A dalilin waka marigayin ya ziyarci kasashe irin su Amurka da Jamaica da Cuba da Bahamas da Brazil da benezuela da Bahrain da Bulgeriya da Romaniya da Ingila da Jamus da sauransu.
Majalisar dinkin Duniya ta taba ba shi lambar yabo ta ‘Zaman Lafiya’ sakamakon wakokin da ya yi na kiran a zauna lafiya, sannan ya samu lambobin yabo daban-daban a kasashen da ya yi waka.
What's new in the latest 1.0
Dan Maraya Jos APK -informatie
Supersnel en veilig downloaden via de APKPure-app
Eén klik om XAPK/APK-bestanden op Android te installeren!