Wannan fassarar littafin Ahdhari ne wanda ke bayani kan ibada a Musulunci.
Godiya ta tabbata ga Allah Madaukakin Tsarki, Tsira da Amincin Allah su kara tabbata ga fiyayyen halitta Annabi Muhammad (SAW) bayan haka, Wannan Fassarar Littafin Ahdhari ne cikin harshen Hausa, domin amfanin Musulmi kasancewar wannan hanya mafi sauki wajen yada sako a cikin fadin duniya ga miliyoyin mutane, sabanin tsohuwar hanya ta buga littafi a rarraba shi, da fatan za’a samu Wani wanda zai dauki nauyin wannan aiki a matsayin Sadakatul Jariya domin cigaba da gudanar da wannan aiki na alkhairi ta yadda wata rana zai zamanto akwai tarin littattafai masu yawa cikin harshen Hausa. ina kuma aiki kan update a yanzu dan ya zama daidai da app di na, na Hajj da Umrah domin dada saukaka shi ga mai karatu.