About Mallam Sa'idu Haruna Kano Full
Karatun AlQur'ani Mai Girma na Mallam Sa'idu Haruna Kano State - Nigeria.
Mallam Sa'idu Haruna Kano shi ne wanda ya ke jan bakin AlQur'ani mai girma a tafsiran da marigayi Sheikh Ja'afar Mahmud Adam Kano yake gabatarwa duk shekara a masallacin Alhaji Muhammadu Indimi da ke Damboa road, Maiduguri, Borno State - Nigeria.
Bayan shahadar da Sheikh Ja'afar ya samu a asubahin ranar jumu'a 13th April, 2007 a sakamakon gisan gillar da yan bindiga suka yi masa na harbi da harsashan bindiga, mallam Sa'idu ya ci gaba da ja wa Sheikh Dr. Muhammad Sani Rijiyar lemo baki a masallacin indimi, kana daga bisani yanzu haka yana jan baki wa Sheikh Dr. Bashir Aliyu Umar a masallacin Al_Furqan dake cikin birnin Kano.
Shi kuma Dr. Rijiyar lemo ya koma tafsirinsa a masallacin Gwallaga dake Bauchi State - Nigeria.
Allah Ya saka wa malamanmu da alkhairi.
Shi kuma Sheikh Ja'afar da Albani Zaria da Dan maishiyya Sokoto da aka hallaka a fagen da'awah , Allah Ya ji kansu da rahama. Ya sa aljanna ce makomarsu.
Da fatan za ku ji dadin sauraro wannan application.
Mu na fatan kuma ku sanya mu a addu'a.
Wassalam alaikum.
What's new in the latest 1.0
Mallam Sa'idu Haruna Kano Full APK Information
Old Versions of Mallam Sa'idu Haruna Kano Full
Mallam Sa'idu Haruna Kano Full 1.0

Super Fast and Safe Downloading via APKPure App
One-click to install XAPK/APK files on Android!