皖南应用嚣雅昆石华数达加cikin fitattun wakokin ALH穆萨Dankwairo。
A takaice an haifi Alh. Musa Dankwairo a shekarar 1907 a garin Bakura wanda tsakanin Bakura da Sokoto, akwai tazarar kilomita 105. Sunan Mahaifinsa usman Dankwanda. Shi Usman Dankwanda ya rayu a Kaya ne kuma yana yiwa sarkin Kayan Maradun Waka, Mahaifin Dankwairo da kakansa duk makadan sarkin kayan Maradunne. Ya tashi ya tarar da kakansa da Mahaifinsa suna waka tare, amma ya fi rayuwa da mahaifinsa rayuwa ta hakika. Kuma tun yana Dan shekara 6 zuwa 7 mahaifinsa ya ke zuwa da shi a cikin tsangaya ta waka, sabanin irin su Dandada Aliyu mai-taushi da Na-rambada da gaba daya basa zuwa da Yayansu, su sun dauki waka kaddarace ta shigar da su shi ya sa basa son Yayansu su gaje su.