Tarihin Annabi Muhammad S.A.W

Tarihin Annabi Muhammad S.A.W

Abrahamjr
Aug 2, 2024
  • 17.6 MB

    File Size

  • Android 4.4+

    Android OS

About Tarihin Annabi Muhammad S.A.W

Cikakken Tarihin Fiyayyen Halitta Annabi Muhammad (S.A.W)

Manzo Muhammad Al-Habib ɗan Abdullahi (Sallallahu alaihi wa sallam).

Muhammad ɗan Abdullahi ɗan Abdul-Muɗallibi ɗan Hashimi ɗan Abdu-Manafi ɗan qusayyi ɗan Kilabi, Sallallahu alaihi wa aalihi wa sallam,

(Harshen Larabci: Abūl-Qāsim

Muḥammad ibn AbdAllāh ibn Abd al-Muṭṭalib ibn Hāshim ibn Abd Manāf ibn Qusayy ibn Kilāb) nasabarsa maɗaukakiya tana tuqewa zuwa ga Annabi Ibrahim, alaihi salatu wassalam.

Mahaifiyarsa: Ita ce Aminatu (Aminah) ‘yar Wahbi ɗan Abdul-Manaf ɗan Zuhrata ɗan Kilabi (Radhi yAllahu anhuma).

Alkunyarsa: Abul-Qasim, Abu Ibrahim.

Laqabinsa: Almusɗafa yana da sunaye da suka zo a cikin Kur’ani mai girma kamar, Khataman nabiyyin, da Al’ummi da Almuzzammil da Almuddassir da Annazir da Almubin da Alkarim da Annur da Anni’ima da Arrahma da Al’abdu da Arra’uf da Arrahim da Asshahid da Almubasshir da Annazir da Ad’da’i da sauransu.

Tarihin haihuwarsa: 17 Rabi’ul Auwal Shekarar Giwa (571m) bisa mash’hurin zance gun Ahlul Baiti (a.s), an ce, 12 ga watan da aka ambata.

Wurin haihuwarsa: Makka.

Aikoshi: An aiko shi a Makka 27 Rajab yana ɗan shekara arba’in.

Koyarwarsa: ya zo da daidaito tsakanin dukkan halitta da ‘yan’uwantaka da rangwame na gaba ɗaya ga wanda ya shiga musulunci, sa’annan ya kafa shari’a maɗaukakiya da dokoki na adalci da ya karɓo daga wajan Allah (swt) su kuma musulmi suka karɓa daga gare shi.

Mu’ujizozinsa: Mu’ujizarsa maɗauwamiya ita ce Kur’ani amma waɗanda suka faru a farkon Musulunci suna da yawa ba sa kuma kirguwa.

Kiransa: Ya kira mutane zuwa ga Tauhidi a Makka a ɓoye shekara uku ya kuma kira su a bayyane shekara goma.

Hijirarsa: ya yi hijira daga Makka zuwa Madina a farkon watan Rabi’ul Auwal bayan shekara 13 daga aikensa, wannan ya faru ne sakamakon cutarwa daga kafirai gare shi da kuma ga sahabbansa.

Yaqoqinsa: Allah ya yi wa Manzo izinin yaqar mushirikai da kafirai da munafukai, sai ya yi ɗauki ba daɗi da su a wurare da yawa da mafi girmansu sune: Badar- Uhud- Al-khandak (Ahzab)- Khaibar- Hunaini.

Matansa: KHadija ‘yar Khuwailid (a.s) ita ce matarsa ta farko, amma sauran su ne: Saudatu ‘yar Zami’a da A’isha ‘yar Abubakar da Gaziyya ‘yar Dudan (Ummu Sharik) da Hafsa yar Umar da Ramla ‘yar Abu Sufyan (Ummu Habibia) da Ummu Salama ‘yar Abu Umayya da Zainab ‘yar Jahash da Zainab ‘yar Huzaima da Maimuna ‘yar Al-Haris da Juwairiyya ‘yar Al-Haris da Safiyya ‘yar Huyayyi ɗan Akhdabl.

‘Ya’yansa:

1-Abdullah

2-Al-Qasim

3-Ibrahim

4-Faɗima (a.s) a wani qaulin da Zainab da Ruqayya da Ummu Kulsum.

Ammominsa: su Tara (9) ne, su ‘ya’yan AbdulMuɗallib ne: Al-haris da Zubair da Abu ɗalib da Hamza da Al-Gaidak da Dirar Al-muqawwam da Abu Lahab da Abbas.

Ammominsa mata: Su shida (6) ne daga iyaye mata daban-daban su ne: Amima da Ummu Hakima da Barra da Atika da Safiyya da Arwa. Wasiyyansa goma sha biyu ne, su ne: Amirulmuminina Ali ɗan Abi ɗalib (a.s) da Hasan ɗan Ali da Husain ɗan Ali da Aliyyu ɗan Husaini da Muhammad ɗan Ali da Ja’afar ɗan Muhammad da Musa ɗan Ja’afar da Ali ɗan Musa da Muhammad ɗan Ali da Ali ɗan Muhammad da Alhasan ɗan Ali da Muhammad ɗan Hasan Mahadi (a.s).

Mai tsaron qofarsa: Anas ɗan Malik.

Mawaqinsa: Hassan ɗan Sabit, da Abdullahi ɗan Rawahata, da Ka’abu ɗan Malik.

Mai kiran sallarsa: Bilal Al-Habashi da Abdullahi ɗan Ummu Maktum da Sa’ad Al-kirdi.

Tambarin zobensa: Muhammadur Rasulullah

Tsawon rayuwarsa: shekaru 63.

Tsawon lokacin Annabtarsa: shekaru 23.

Tarihin wafatinsa: 28 Safar 11 H.

Wajan da ya yi wafati: Madina.

Inda aka binne shi: Madina a Masallaci Maɗaukaki Mai alfarma.

Show More

What's new in the latest 10.1

Last updated on Aug 2, 2024
Minor bug fixes and improvements. Install or update to the newest version to check it out!
Show More

Videos and Screenshots

  • Tarihin Annabi Muhammad S.A.W poster
  • Tarihin Annabi Muhammad S.A.W screenshot 1
  • Tarihin Annabi Muhammad S.A.W screenshot 2
  • Tarihin Annabi Muhammad S.A.W screenshot 3
  • Tarihin Annabi Muhammad S.A.W screenshot 4
  • Tarihin Annabi Muhammad S.A.W screenshot 5
  • Tarihin Annabi Muhammad S.A.W screenshot 6
  • Tarihin Annabi Muhammad S.A.W screenshot 7

Tarihin Annabi Muhammad S.A.W APK Information

Latest Version
10.1
Android OS
Android 4.4+
File Size
17.6 MB
Developer
Abrahamjr
Available on
Safe & Fast APK Downloads on APKPure
APKPure uses signature verification to ensure virus-free Tarihin Annabi Muhammad S.A.W APK downloads for you.

Old Versions of Tarihin Annabi Muhammad S.A.W

APKPure icon

Super Fast and Safe Downloading via APKPure App

One-click to install XAPK/APK files on Android!

Download APKPure
thank icon
We use cookies and other technologies on this website to enhance your user experience.
By clicking any link on this page you are giving your consent to our Privacy Policy and Cookies Policy.
Learn More about Policies