Makarantar Soyayya
About Makarantar Soyayya
Ina Masoyan Asali, Soyayya dadi tafi zuma dadi!!!
Akwai wata magana ko karin magana da masoyan asali suke fadi akan soyayya, wato SOYAYYA dadi tafi zuma dadi! wannan haka yake tabbas babu abin da yafi so dadi a rayuwa inkasameshi ke ko kai da masoyinki ko masoyiyarka ka chaba, haka zalika kema kincaba.
Soyayya fa halitta neh kuma kamar yadda ubangiji ya haliccemu maza da mata yasanya wannan halintan a zuciyarmu wato halittar so.
Wannan manhaja mai suna Makarantar soyayya ya qunshi kalamai da rubuce rubuce masu dadi da mahimmanci akan soyayya, so, kauna da sauransu. Iya kalaman soyayya da cika alqawari da kula da junanku amatsayinku na masoya shi ne zai qara danqon soyayyanku.
wasu daga cikin kalaman soyayyan da yakamata kina fadi masa ko kana fadiwa masoyiyarka sunhada da
Amincin Allah da kariyarsa da yaddarsa su tabbata ga sarauniyar kyawawa. Tauraruwa mai haskaka duniya. Gani nazo gareki ko na samu jin daddadan kalamanki masu sanya nutsuwa ga mai sauraro. Sannan naga kyakkyawar surar da Allah ya baki wadda ke samar da farin ciki da nishadi ga mai kallo. Taku kike tamkar sarauniya, ina so nayi amfani da wannan damar na bayyana miki yadda sonki yake a cikin zuciyata, sonki yabi jijiya ya ratsa tsoka ya fasa kashi da bargo da ke nake rayuwa sonki shi ne ya zamto jinin jikina. Yabonki shi ne abincina begenki shi ne ruwan shana, kaunarki ita ta zamto min numfashi na, my one ba zan iya rayuwabaa idan babu ke kece farin ciki na da tunaninki nake kwana da yabonki nake tashi da zancenki nake yini duk motsina naki ne kece farin cikin zuciya ke ce abar alfaharina kece kadai idaniyana ke iya gani, ki tallafawa dan marayan da ya rasa duk wani farin ciku don ganin ya sameki. Kece kadai zaki iya dawomin da farin ciki na da walwalata da dariyata idan kikace bakya sona zan rasa rayuwata.
Zuwa ga bakuwar zuciya mai kyakkyawar fuska hadi da kyakkyawan suna mai dadin kamshi mai kyakkyawan Murmushi mai zazzakar murya, ita ke sani na manta komai. Haka kyawawan idanuwanki sukansa na zamanto makaho a yayin da suka yo arba da kyakkyawar mace tana kusanto almajirinta, idan naji an kira sunanki sai naji wani nishadi tamkar an yimun albishir da aurenki, duniyar masoya kizo muyi shigewa ki sani a hannun dama domin jini da jijiya hadi da duk kaina farin ciki na idan na tunaki sai naji wani shauki ko aiki ki yarda da ni ki sani a cikin zuciyarki sarauniyar mata.
What's new in the latest 1.0.0
Makarantar Soyayya
So
Makarantar Soyayya APK Information
Old Versions of Makarantar Soyayya
Makarantar Soyayya 1.0.0
Super Fast and Safe Downloading via APKPure App
One-click to install XAPK/APK files on Android!